Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta samu labarin cece-kuce da ya biyo bayan wa’azin da Malam Abubakar Lawan Triumph ya gabatar, wanda ya janyo muhawara da damuwa daga wasu kungiyoyi. Ko da yake ana da ‘yancin fadin albarkacin baki da ‘yancin addini, rundunar tana da alhakin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin al’umma.
A kokarinta na shawo kan lamarin, ranar 10 ga Yuli, 2025, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano ya gayyaci Malam din, inda aka fara tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki ciki har da jami’an gwamnati, shugabannin addinai, da wakilan al’umma domin duba batun da daukar matakan da suka dace domin hana rikici ko wata tangarda.
Saboda haka, rundunar ‘yan sanda tana rokon jama’a da su kwantar da hankali tare da guje wa duk wani abu da zai iya haddasa hargitsi. Muhimmin abu ne a mutunta ‘yancin kowa da ra’ayinsa, da kuma bin doka da oda wajen gudanar da addini ko bayyana ra’ayi.
Rundunar tana karfafa gwiwar duk wanda ke da korafi ko wata damuwa da ya nemi hanyoyin da suka dace na shigar da rahoto, maimakon yin amfani da kafafen sada zumunta wajen yada kalaman da ka iya haddasa rikici ko tayar da husuma.
Hedkwatar ‘Yan Sandan Jihar Kano na tabbatar da aniyar ta na ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da doka da oda a cikin jihar, tare da mutunta ‘yancin kowane dan kasa ba tare da la’akari da asalinsa ko bangaren da ya fito ba.
"Muna kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da hadin kai wajen samar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’umma."