Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan abin da ya kira watsi da yankin arewacin Najeriya, inda ya ce shugaban ya fi mayar da hankali kan gina kudancin ƙasar ta hanyar amfani da albarkatun ƙasar.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wajen taron shawarwari na masu ruwa da tsaki kan gyaran kundin tsarin mulkin ƙasa a jihar Kano na 2025 - wanda aka gudanar da yammacin jiya Alhamis.
"Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan," in ji Kwankwaso.
Kwankwaso wanda ya yi wa jam'iyyar NNPP takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya zargi jam'iyyar APC da karkatar da albarkatun ƙasa tsakanin ɓangarori biyu na Najeriya.
Ya ce: "Bari in bai wa waɗanda ke ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa wajen ɗaukar komai, su tuna cewa wasu batutuwan da muke ciki a ƙasar nan a yau suna da alaƙa da rashin isassun kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da wasu ke yi," in ji Kwankwaso.
Ya ce wannan ya sa ake fama da rashin tsaro da talauci da sauransu.
Kwankwaso ya ce yawancin hanyoyi da ke arewacin suna cikin mawuyacin hali, wasu ma sun lalace - a daidai lokacin da gwamnatin APC ke ci gaba da ware maƙudan kuɗaɗe wa ɓangaren ayyukan more rayuwa a kudancin ƙasar.
Ya buƙaci gwamnatin Tinubu da ta sauya alkibla domin tafiya da kowa da kuma tabbatar da cewa an raba albarkatun ƙasa yadda ya kamata domin ci gaban dukkan sassan ƙasar.
"Yanzu lokaci ne da ya kamata gwamnati ta kawo sauyi, domin mu san cewa ba gwamnati ce kaɗai ta wani ɓangare guda ba," in ji shi.