1-An ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu a Najeriya don makokin Marigayin
2-An kafa Kwamitin Manyan Jami'an gwamnati don tsara jana'izar girmamawa ga tsohon shugaba Buhari wanda sakataren gwamnatin tarayya Sen. George Akume ya jagoranta.
3-An dage taron Majalisar Zartarwa ta Kasa daga gobe zuwa juma'a don zaman makoki
4 An umarci mambobi 25 na Majalisar Zartarwar da su wuce Daura don halartar jana'izar zaman makoki na kwanaki uku
4-An ayyana kwanaki 7 na zaman makoki a ilahirin Najeriya tare da yin ƙasa-ƙasa da tutar kasar
5- Babbar tawaga karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa na can na kammala shirye-shiryen kawo gawar da iyalan mamacin gida
6- Za a yi takaitaccen faretin Sojoji a filin jirgin sama na jahar Katsina don tarbar gawar.
7- Za a yi Sallar Jana'iza da rufe gawar a Daura.
8 An bude shafin karbar ta'aziyya a dukkan ma'aikatun gwamnatin tarayya, da na hukumomi, da ilahirin ofisoshin jakadanci na Najeriya da ke kasashen waje.
9- Ana sa ran isowar gawar Katsina da karfe 12 na rana ranar Talata.
10- Za a yi Jana’iza a ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025.
10- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai karbi gawar tsohon shugaban kasa a Katsina tare da manyan baƙi