Daga Baba Ahmad Yunus Sharada
Wannan na cikin rahoton haɗin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya WHO da asusun tallafawa ƙananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF suka fitar kan tsaftar muhalli a nahiyar Afirka.
Haka binciken yace ƴan Najeriya na gaba-gaba cikin jerin kasashen afirka da suka fi gudanar da bahaya a fili.
Sai dai wasu mazauna Kano sun bayyana takaicinsu musamman da jama'ar Najeriya da suka zama na 18 cikin jerin masu gudanar da bahaya a fili.
Inda suka nemi mahukunta da su sabinta dokar hana yin ba haya a fili, ko dan samun ingatacciyar lafiya, da shakar iska mai inganci.