Jami'ar North West a Kano ta dage jarabawar da za'a fara yi a yau talata sabida Zanga-zangar kungiyar ASUU
Jami’ar Northwest da ke Kano ta sanar da dage jarabawa saboda zanga-zangar da Æ™ungiyar ASUU ta shirya gudanarwa a ranar, Talata 26 ga Agusta, 2025.
Sanarwar da shugaban sashen hulÉ—a da jama’a na jami’ar, Abubakar Ibrahim, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa jarabawar da aka shirya gudanarwa a ranar Talata 26 ga Agusta, yanzu za a yi ta ne a Laraba 27 ga Agusta, 2025.
Haka kuma jarabawar da aka tsara ranar Laraba 27 ga Agusta, za a sake yin ta ne a Litinin 22 ga Satumba, 2025.
Jami’ar ta shawarci É—alibai su lura da wannan canjin jadawalin domin kauce wa rudani.