KAROTA a Kano ta musanta zargin jami'anta sun sace wa wani A.S Bawa kudi a motar sa
Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta musanta zargin wani mutum mai suna A.S. Bawa da ya ce an sace masa kuÉ—i har naira dubu 950 daga cikin motarsa a hannun jami’anta.
Hakan na cikin sanarwar da mai taimakawa shugaban hukumar kan harkokin yaÉ—a labarai Mu’azzam Mansur Kurawa, ya fitar a ranar Litinin, 25 ga Agusta, 2025 a Kano.
Sanarwar ta bayyana cewa an kama Bawa da karya dokokin zirga-zirga bayan ya ajiye motarsa a wajen da bai dace ba, inda jami’an KAROTA suka É—auke ta zuwa shalkwatarsu, bayan an yi masa neman duniya an rasa.
Hukumar ta ce lokacin da Bawa ya zo, ya garzaya shalkwatar, inda ya rika zagi da kalaman batanci ga jami’an da ya samu, yana yi musu barazana.
Daga baya ya aika wakilai biyu don su duba motar, inda suka buÉ—e ta a gaban jami’an ’yan sanda da wasu shaidu.
Sanarwar ta Æ™ara da cewa Bawa ya yi ta sauya magana kan adadin kuÉ—in da yake zargin sun É“ace daga cikin motar, daga farko ya ce ₦350,000 ne, daga baya ₦500,000, sannan daga Æ™arshe ya ce ₦950,000 kamar yadda ya rubuta a Æ™orafinsa ga ’yan sanda.
KAROTA ta musanta cewa jami’anta sun taÉ“a dukiyarsa, tare da bayyana mamakinta kan yadda mutumin da ya ce lauya ne zai sauya magana ta hanyoyin da za su iya tozarta darajar lauyoyi.