Wata majiya daga Majalisar ta tabbatarwa da TST Hausa cewa Majalisar na cigaba da tattaunawa da muhawara kan matakin da za’a dauka kansa.
Majiyar ta shaida cewa an dauki matakin saboda zargin Shugaban karamar hukumar da sayar da tsohuwar kasuwar Rano.
TST Hausa ta kuma rawaito cewa ana zargin Shugaban karamar hukumar da aka dakatar da sayar da takin zamani na noma da gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya rabawa kananan hukumomin kano a watan Yulin da ya gabata.
Ko wacce karamar hukuma ta samu tirela uku na takin zamanin mai dauke da buhu 600 ko wacce mota