Daga Hafsat Muhammad Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci zaman majalisar zartaswa ta ƙasa a fadar shugaban ƙasa a yau Laraba.
Daga cikin manyan jami'an gwamnati da su ka halarci zaman sun haɗa da Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack, Shugaban Ma’aikata na Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, da Mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu.
Suma ministoci da yawan su sun halasci zaman.
A zaman an tattauna batutuwa masu muhimmanci ga ƙasa.