Abdulmumin Jibrin Kofa, makusanci ga Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP, ya sake ganawa da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Villa, Abuja, a ranar Lahadi — karo na biyu cikin makonni biyu.
Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta dauki tsawon sa’o’i biyu, inda ake kyautata zaton ta shafi dangantakar Tinubu da Kwankwaso da kuma karuwar adawa ga jam’iyyar APC a wasu yankunan arewacin Najeriya.
Jibrin, wanda ya ki bayyana dalilin tattaunawar, ya yi ganawa ta farko da Tinubu a ranar 30 ga Yuli, inda ya ce sun tattauna kan dunkulewar kasa da ci gaban ta.
Ganawar ta na zuwa ne kwanaki bayan zargin Kwankwaso cewa gwamnatin tarayya na fifita kudu a ayyukan ci gaba.
Wasu majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar wa da jaridar TheCable cewa ganawar na da alaka da batun alakar Kwankwaso da Tinubu.