Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar PDP, Malam Ibrahim Shekarau, ya jaddada cewa hadakar jam’iyyu kai tsaye ita ce hanyar kawar da gwamnatin Tinubu a 2027 ba ta É—aiÉ—aikun mutane ba.
Shekarau ya ce ba a fahimci maganganunsa na baya ba kan haÉ—akar wasu Æ´an siyasa a karkashin jam’iyyar ADC domin kwace mulki daga hannun APC.
Ya bukaci dukkan jam’iyyun adawa da su binciko hanyoyi da dabarun farfaÉ—o da dandalin siyasa domin cimma wannan buri, inda ya bayar da misalin yadda shi da wasu Æ´an kishin Æ™asa suka yi Æ™oÆ™arin kafa haÉ—aka a 2011 domin kifar da tsohon shugaba Goodluck Jonathan daga mulki.