Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta bayyana damuwa kan yadda ake samun ƙananan yara na tuƙa Adaidaita Sahu a cikin birnin Kano, lamarin da ta ce ya janyo haɗura guda 16 a watan Agusta, 2025, tare da jikkata mutane da lalata dukiyoyi.
Wannan na cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a madadin Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori.
Rundunar ta tunatar da cewa hana ƙananan yara tuka Adaidaita Sahu ya zama dole ne domin guje wa haɗura.
Ta yi gargaɗin cewa iyaye da mamallaka baburan za su fuskanci hukunci idan aka kama ’ya’yansu ƙanana suna tuka Adaidaitar.
Rundunar ta kuma gargadi dukkan masu ababen hawa da su kiyaye dokokin zirga-zirga, tare da jan hankalin cewa za a cafke kuma a gurfanar da masu karya doka a kotu.