Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Jihar Sokoto kuma tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Aminu Waziri Tambuwal, kan zargin almundahanar naira biliyan 189.
Bisa ga rahotanni, an kama Tambuwal ne a yau yayin da ake gudanar da bincike kan yadda aka yi amfani da kudaden gwamnatin jihar a lokacin mulkinsa.
Majiyoyi daga hukumar EFCC sun tabbatar da cewa an tsare shi domin gudanar da cikakken bincike, yayin da ake ci gaba da samun ƙarin bayani game da lamarin.
EFCC ba ta bayar da cikakken bayani kan matakin da za ta É—auka ba, sai dai rahotanni sun ce ana ci gaba da bincike kafin yanke hukunci.