Alarammomi da malamai masu kula da tsangayun Alkur’ani a Jihar Kano sun nemi Gwamnatin Kano ta tabbatar da kulawa ta musamman ga tsangayun karatun Alkur’ani a fadin jihar.
Wannan na cikin sanarwar da Kungiyar Tsangaya Abar Alfaharinmu ta fitar mai dauke da sa hannu Shuagbanta Alaramma Muhammad Sani Musa Nuhu (Sanin Malam).
Ya ce, suna neman a saka wakilin tsangayu a cikin Majalisar Koli ta Malamai da aka kafa, a samar da fitulun sola a dukkan tsangayu, a dinga ware musu kaso a kasafin kudin kowace shekara, da kuma gina rumfunan karatu, bandakuna da dakunan kwana ga almajirai.
Sauran bukatun sun hada da samar da ruwan sha, muhalli na dindindin, karrama fitattun alarammomi, sanya almajirai cikin shirye-shiryen koyon sana’a da raba jari da kuma samun kaso a tallafin takin zamani.
Sanarwar ta kuma yi godiya ga Gwamnan kan nadin Gwani Musa Falaki a matsayin mai taimakawa gwamna kan harkar tsangayu, tare da jinjina wa tsohon Gwamna Kwankwaso bisa ɗaukar nauyin koyar da almajirai kyauta.