NAHCON ta sanya N8.5 Miliyan a matsayin kuɗin aikin Hajji na 2026
Hukumar kula da aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ayyana cewa kudin aikin Hajji na shekarar 2026 zai kasance Naira miliyan 8.5 a matsayin kuɗin da maniyyata za su fara ajiyewa.
A cewar sanarwar da Mataimakiyar Daraktar Sashen yaɗa Labarai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar, an bayyana kudin ne bayan taron bitar aikin Hajjin 2025 da aka yi tare da shugabanni da sakatarorin hukumomin jin dadin alhazai na jihohi.
Ta ce za a daddale cikakken kuɗin aikin Hajji na badi bayan kammala tattaunawa kan dukkan kwangilolin ayyuka.
Usara ta kara da cewa Saudiyya ta sake bai wa Najeriya guraben alhazai 95,000 kamar yadda aka saba, kuma rabon kujeru ga hukumomin jin dadin alhazai na jihohi ya tsaya yadda yake a bara.
Ta rawaito Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, na gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayansa ga alhazai da kuma hukumar.