Ƴan Najeriya Dubu 24 ne suka bata daga 2024 zuwa 2025 sanadiyyar Boko Haram -- Red Cross
Akalla kusan mutum Dubu 24 ne kungiyar bayar da agaji ta Duniya Red Cross ta ce sun bata a dalilin rikicin makayan Boko Haram a Najeriya.
Dubban mutanen wadanda ake hasashen kusan kashi 80 zuwa 90 dinsu 'yan Arewa ne, kungiyar ta ce kawo yanzu ba'a san ainihin inda suke ba.
Red Cross ta kum bayyana takaicinta karara kan yadda matsalar tsaron ke dai-daita rayuwar Al'umma tare da raba da dama daga muhallansu.