Babban Faston Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adejare Adeboye, ya sake bayyana hasashe kan yadda zai rabu da duniya.
Ya ce zai mutu cikin lumana, a ranar Lahadi, bayan ya halarci cocin kuma ya ci sakwara, abincin da yafi so.
Da ya ke jawabi a rana ta huÉ—u na babban taron cocin na kasa da kasa mai taken “The Overcomers”, Fasto Adeboye ya jaddada cewa mutuwa ba sai da ciwo ba.
Faston ya taba bayyana wannan hasashen shekaru biyu da suka gabata, inda ya ce: “Zan mutu ne a ranar Lahadi, bayan na halarci coci, na ci sakwara da nake so, sannan in rabu da duniya ba tare da wani ciwo ba.”
Faston ya ce mutuwarsa za ta kasance ta gaggawa kuma salin-alin zai mutu.