Ƴan Dabar zango da kofar mata dake Kano sun raunata dabbobi a Kasuwar Rimi ta hanyar caccaka musu wuka
Gungun ƴan daba dake rikicin fadan Daba na Unguwannin Zango da Kofar Mata sun raunata dabbobi da dama a Kasuwar Rimi da ke Kano duka dai a yankin karamar hukumar birnin Kano, ta hanyar sukar su da wuƙaƙe.
Wasu daga cikin masu dabbobin sun shaida wa Raihana cewa, ƴan daban sun raunata Dokuna, Shanu, Awaki, da Tumaki a kasuwar.
Yankin Zango da Yakasai dai na cikin yankunan da faɗace-faɗacen daba ya yi ƙamari a Kano.
Wanda haryanzu hukumomi sun gaza kawo karshen wannan fadan, ko a satin daya gabata daruruwan mata da kanan yarane suka fito Zanga-zanga a Unguwar Kofar mata da Unguwar zango neman daukin mahukanta na kawo karshen fadace-fadacen Daba.