Good luck Jonathan ya yiwa Peter Obi tayin takarar minista idan ya janye daga takara ya mara masa maba -- Kachikwu
Tsohon É—an takarar shugaban Æ™asa na jam’iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban Æ™asa, Goodluck Jonathan, ya yiwa Peter Obi, tayin kujerar ministan harkokin tattalin arziki idan ya janye daga takara, ya goyi bayansa.
Kachikwu da ya faÉ—i haka a wani taron manema labarai ranar Juma’a a Abuja, ya yi zargin cewa wasu Æ´an siyasa daga Arewa ne suka shigo da tsohon shugaban Æ™asa Jonathan cikin takarar shugaban Æ™asa domin raunana siyasar Kudu.
Kachikwu ya Æ™ara da cewa an shaida wa Obi cewa ba zai iya samun kuri’un Arewa ba saboda shi É—an kabilar Ibo ne.