Ɗan takarar gwamnan Kano a jamʼiyyar ADC 2023, Malam Ibrahim Khalil ya ce zai ci gaba da yin takarar gwamna a jihar Kano har sai ya cimma burinsa.
Ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai, bayan da yan siyasa ke ci gaba da shiga jami'iyyar ta ADC.
Sheikh Khalil wanda ya taɓa yin takarar gwamnan Kano sau ɗaya, da kuma takarar neman zama ɗan takara gwamna a baya, ya kasance cikin waɗanda suka fi samun ƙuri'u a zaɓen 2023, a bayan jam'iyyun NNPP da APC da kuma PDP.