Daruruwan matasa ne a yankin Gwagwarwa dake Karamar hukumar Nassarawa suka fito Zanga-zangar lumana, domin kira ga Jagoran Gwamnatin Kano Alh. Abba Kabir Yusuf da ya ceto yanki, wajen damkawa Jagoran yankin Barr Isah Ibrahim "Matawallen Gwagwarwa".
Matansa da suka hadar da Maza da Mata sunfito sama da 800 suna kira ga maigirma Gwamna cewar, Matawallen Gwagwarwa shi kadaine wanda yake amsa koken matasan yanki,
Kamar yadda wanda ya jagoranci matasan Kamilu Gwagwarwa ya shaidawa Jaridar Raihana a wannan rana ta Alhamis, ya ce Barr ya bawa matasan yankin jari, ya samar musu da abun yi, don haka suke san Gwamnan Kano da ya wai-wayo gareshi domin ya cigaba da habbaka rayuwar matasan yanki.
A karshe Kamilu Gwagwarwa ya ce suna kira ga Gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf da ya yiwa Allah da Ma'aiki ya amsa kokensu, ya bawa Barr Isah Ibrahim babbar kujerar da zai cigaba da inganta rayuwar mazauna yankin.