Sultan ya sanar da Litinin a matsayin 1 ga watan Rabi'ul Awwal
Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar ƙoli ta harkokin addinin Musulunci, Muhammad Sa'ad Abubakar ya sanar da gobe Litinin a matsayin 1 ga watan Rabi'ul Awwal.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa daga Wazirin Sakkwato kuma shugaban majalisar shawarwari ta fadar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Junaidu a juya Asabar.
Ya ce sanarwar, wacce aka yi ta da hadin gwiwar kwamitin duban wata, ta zo ne biyo bayan kasa ganin jaririn watan na Rabi'ul Awwal a jiya Asabar.