Tsofaffun Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Barranta Kansu Da Maganganun Shugaban APC Kano
Abdullahi Abbas
Shugaban kungiyar tsofaffun kansilolin Jam'iyyar APC wanda wasun su suka sauya sheka daga Jam'iyyar ta APC zuwa NNPP sun, musanta maganar da shugaban Jam'iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas ya yi na cewar sun turo su ga gwamnan Kano Abba Kabir Yusif ne domin su yi musu yakin sunkuru a siyasa da cewa ba gaskiya bane, shiftin Gizo ne kawai.
Sunusi Kata Madobi wanda shine shugaban kungiyar ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaki na musamman da tsofaffin kansilloli sama da 3000 suka gudanar cikin ma'aikatar yaÉ—a labarai da ayyukan cikin gida a sakatariyar Audu Bako.
Ya kuma ce, za su sakawa gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da halarci bisa halarcin da ya yi musu na maida su mutane.
Wasu daga cikin tsofaffun kansilolin da suka halarci taron sun bayyana mubaya'ar su ga gwamnan na Kano.
Ita a nata bangaren Hajiya Uwa Magaji Jiki Daga Bebeji tace mu kansilloli ne ba yaran Abdullahi Abbas bane don haka magana da yake yi cewar sun turo mu wanke gara ne, wannan ba gaskiya bane, kyawawan halayen gwamna Abba ne suka jawo hankalin su suka zo Cikin inuwarsa.
Shima Dahiru Yusuf daga Gezawa kuma tsohon kansila yace shima yana cikin wadanda tsohuwar gwamnatin Danduje ta hana hakkin su, don haka maganar Abdullahi Abbas ba gaskiya bane! Sun ga gwamna Abba zai jikan mu ne shine suke neman bata mana ruwa.
Da yake mayar da martani kan ziyarar da suka kai musu yace, mai girma Gwamna ya amince da cewar zai biya su hakkokin wanda gwamnatin baya ta kasa biyansu, kuma gwamnan yace baya bukatar sakamakon komai daga gare ku wai don ku koma jam'iyyar sa, a a yayi ne domin Allah.
Gwamnan yace magana ake ta Kano kawai kuma ku yan Kano ne, don haka maganar da Abdullahi Abbas yayi magana ce wadda girmansa da darajarsa ta wuce ace yana irin wadannan abubuwan nan idan dai mai kaunar Kano ne shi.
Don haka muna muku fatan alheri da fatan kowa zai koma gidansa lafiya bisa ziyarar jaddada mubaya'ar su ga gwamnatin ta Kano yau Alhamis.
A karshe dubban tsofaffin kansillolin wanda suka yi tattaki dauke da kwalaye da rubuntun barranta kansu da Kalaman Shugaban jamiyyar APC na jihar kano sun kewaya cikin sakatariyar Audu bako zuwa ma'aikatar ƙananan hukumomi domin nuna goyon bayansu ga ayyukan Alherin gwamna Abba Kabir Yusuf