Yiyuwar komawar Jonathan Jam'iyyar ADP ne ya hana Atiku karbar katin Jam'iyyar
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya dakatar da shirin karbar katin zama dan jam’iyyar African Democratic Congress ADC, a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai iya shiga takarar shugaban kasa a 2027, kuma jam’iyyar ADC ce ke nemansa.
Atiku, wanda a kwanakin baya ya yi adabo da jam’iyyar PDP bayan da aka dade ana takaddama a cikin gida, shi ne ya tsara sauya shekarsa zuwa ADC.
Jami’an ADC ne za su ba Atiku katin zama mamba a mahaifarsa ta Jada da ke karamar hukumar Jada a jihar Adamawa.
Duk da haka, PUNCH ta tattaro cewa bikin, wanda aka shirya yi a ranar Laraba, 6 ga watan Agusta, an dage shi sai baba ta gani ba tare da wani bayani a hukumance daga ɓangaren tsohon mataimakin shugaban kasar ba.
Haka zalika, wani jigo a jam’iyyar ADC ya shaida wa jaridar PUNCH cewa jam’iyyar ta yi ta tattaunawa da Jonathan kan yiwuwar tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
Da yake zantawa da jaridar, shugaban jam’iyyar ADC reshen jihar Adamawa, Shehu Yohana, ya ce an dage rajistar da Atiku zai yi a jam’iyyar ba tare da wata sabuwar rana ba.
A halin da ake ciki kuma, wani jigo a jam’iyyar ADC a matakin kasa, wanda baya son a buga sunansa, ya shaida cewa dage karbar katin jam'iyyar ba zai rasa nasaba da rigimar iko ba tsakanin Atiku da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi.
Jigon jam’iyyar ya yi zargin cewa tafiyar siyasa ta Obi ta kwace jam'iyyar ADC a Kudu, lamarin da ya ce ya jefa burin Atikun na zama shugaban kasa cikin barazana.