Hukumar kula da lafiyar ababen hawa na Jihar Kano (VIO) ta sanar da Makarantun koyar da tukin mota masu zaman Kansu (Private driving school) cewa za ta fara zagayen duba ingancin Makarantun, domin tabbatar da sun cika ka'idojin koyar da Tuki a jihar Kano.
Haka kuma Hukumar ta sanar da duk wani dalibi da ya gama daukar horo daga waÉ—annan Makarantun cewa ya tabbatar ya ziyarci offishin Hukumar ta ( VIO ) dake hanyar Zaria domin yib gwajin tuki (Driving Test)
Shugaban Hukumar na Jihar Kano Engr. Hassan Garba ya bayyana hakan ya na mai cewa shirin aikin duba Makarantun koyar da tuƙi masu zaman kansu zai gudana domin tabbatar da sun cika ƙaidar koyar da tuƙi a jihar kano.