An gano Gawar Dalibar aikin Jarida Emanuel Kefas a gidan saurayin ta Comfort Jimtop a Jihar Taraba
An gano gawar Emmanuel Kefas, saurayin marigayiya Comfort Jimtop, É—alibar koyon aikin jarida a Jami’ar Taraba, a Æ™auyen Tudiri da ke Æ™aramar hukumar Ardo-Kola, lamarin da ya Æ™ara tayar da hankula a jihar.
Jami’in hulÉ—a da jama’a na rundunar ’yan sandan Taraba, James Lashen, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar.
Ya ce dagacin Tudiri ne ya sanar da ’yan sanda game da gano gawar a ranar Juma’a.
Lashen ya bayyana cewa an samu wayar Tecno a gefen mamacin, inda bayan bincike aka gano hotonsa tare da marigayiya Comfort Jimtop, inda aka ci gaba da bincike aka gano suna da alaƙar soyayya.
Ya ce, an kai gawar zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya (FMC) Jalingo domin yin gwajin autopsy, yayin da ake ci gaba da tattara bayanai daga iyalan mamacin.
Rundunar Æ´an sanda ta ce har yanzu ba a tabbatar da musabbabin mutuwar su ba, shin ko kashe-kai ne, kisa ko haÉ—ari.
Tun da farko, mutuwar Comfort Jimtop ta haddasa zanga-zanga a Jami’ar Taraba da wasu sassan jihar, inda É—alibai da kungiyoyin kare hakkin É—an adam suka bukaci a gurfanar da wadanda ake zargi.
Kefas shi ne babban wanda aka riƙa zargi kafin gano gawarsa.