Ƴan sandan Kano sun kama wadanda ake zargi da yunkurin kisa a Legos
Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta kama mutane biyu da ake zargi da hannu a wani fashi da yunkurin kisa da ya faru a Bera Estate da ke Chevron a birnin Legas.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 20 ga Satumba, 2025.
Sanarwar ta ce an kama Mathew Adewole, mai shekara 25 a Na’ibawa da Mukhtar Muhammad, mai shekara 31 a Unguwa Uku Kano, bayan samun bayanan sirri.
Bincike ya nuna cewa Mathew ya amsa laifin kai wa wani mai suna Lil-Kesh hari a Legas ranar 19 ga Agusta, 2025, inda ya ji masa rauni a wuya tare da tilasta masa ya tura Naira miliyan 2.12 zuwa asusun Mukhtar ta wayar salula.
Rundunar ta ce an mika waɗanda ake zargin ga rundunar ƴan sanda ta Jihar Legas domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a kotu.
Kwamishinan ƴan sanda na Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya jinjinawa jami’an rundunar bisa nasarar, tare da gode wa jama’a bisa haɗin kai wajen bayar da bayanai.