An karrama Abderrahim Ouhida, mai shekara 16 a filin wasa na Santiago Bernabéu, kafin fara wasan Real Madrid da Espanyol a ranar Asabar, a gasar La Liga ta kasar Sifaniya.
Abderrahim Ouhida, ya rasa mahaifansa, da yan uwansa mata biyu, da kakansa, bayan faruwar wata girgizar kasa da ta faru a kasar Morocco a watan Satumbar 2023.
Tun faruwar lamarin, Madrid ta dauki nauyin kula da shi, har ma ya samu damar kasancewa a karamar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.
A gefe guda kuma, Real Madrid ta dauki nauyin karatunsa domin ganin ya samu rayuwa mai inganci kamar kowa..