Ba kokarin Abba Gida Gida ne yasa Kano tazo na daya a NECO din bana ba – In ji tsohuwar Gwamnatin Ganduje
Tsohuwar gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje a jihar Kano ta taya daliban da suka samu nasara a jarabawar kammala makarantun sakandire a Jihar Kano ta NECO ta 2025 ,Inda jihar tayi fice sama da kowacce jiha a Najeriya.
Jihar ta Kano tayi fice a jarabawar ta NECO da aka fitar da yammacin ranar Laraba Inda daliban Kano suka samu nasara musamman a turancin da Lissafi.
Wannan nasara ba wai sakamakon wani mataki na dan lokaci kadai ba ce, illa dai alamar ingantattun jarin da aka zuba a harkar ilimi tun daga zamanin Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.
A wata sanarwa da tsohon kwamishinan Ilimi na Kano Hon. Muhammad Sunusi Kiru ya fitar aka rabawa manema labarai yace Sakamakon jarabawar ya nuna tasirin tsare-tsaren cigaban ilimi da aka aiwatar a wancan lokaci, ciki har da ginawa da gyara makarantun sakandire a Kano da karawa malamai albashi da basu horo, da kuma samar da ingantattun hanyoyin tallafawa dalibai.
Hon. Kiru yace Wannan ne ya kafa tushe mai karfi wanda ya bai wa daliban Kano damar taka rawar gani a yau.
Sanarwar tace don haka, yana da muhimmanci a fahimci cewa wannan nasara ta kasance sakamakon dogon shiri da hangen nesa, ba wai kawai abin da gwamnati mai ci ta yi a dan lokaci kadan ba.
Nasarorin ilimi irin wannan kan kasance sakamakon juriya da cikakken tsari na shekaru da dama.
“Ina taya dalibanmu murna bisa wannan bajintar, tare da yabawa malamai da iyaye kan jajircewar da suka nuna.
Hakazalika, ina godewa gwamnatocin da suka gabata musamman gwamnatin Ganduje da ta samar da ginshikin wannan cigaba”Inji Kiru.
Tsohon kwamishinan na Ilimi amadadin tsohuwar gwamnatin ta Kano yace yana fatan Allah ya sanya wannan nasara ta ci gaba da zama hanyar kara habaka ilimi a Kano domin amfanin zuri’a masu zuwa.