Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sama da shekaru biyu da Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki, babu wata alama da ke nuna zai iya magance matsalar yunwa da talauci da ke addabar ’yan Najeriya.
Atiku ya ce yunwar da ake fama da ita a ƙasar abin kunya ne musamman ga talakawa da marasa galihu.
Ya jaddada cewa mafi yawan juyin juya halin da aka gani a duniya ya samo asali ne daga yunwa da matsin rayuwa, musamman matsalar rayuwa ta kunci a cikin ƙasar da ke da albarkatu.
Atiku cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya fitar a ranar Litinin, ya ce duk da cewa babban aikin kowace gwamnati shi ne tsaron rayuka da walwalar jama’a, al’ummar Najeriya a halin yanzu suna cikin mawuyacin hali na talauci da yunwa a karkashin gwamnatin Tinubu ta jam’iyyar APC.
Ya kara da cewa wannan matsala tana haifar da Æ™arin aikata laifuka irin su damfara, ta’addanci, garkuwa da mutane, É—abi’un ’yan kungiyar asiri, shaye-shaye da maido da al’adu na sadaukar da rayuka.
Ya yi nuni da cewa wannan mummunan yanayi ya zama dama ta yin nazari, inda ya kawo misali da juyin juya halin Faransa, na Rasha a 1917 da kuma “Arab Spring” wanda ya fara daga Tunisia bayan wani matashi ya yi Æ™ona kansa saboda takaicin rayuwa, sannan ya bazu ya girgiza gabashin duniya. A cewarsa, a Najeriya ma za a iya cewa boren EndSARS ya samo asali daga takaicin yunwa da rashin kulawa daga gwamnati.
Atiku ya ce duk da ikirarin gwamnatin Tinubu na yin sauye-sauye, gaskiyar magana ita ce rashin wadatar abinci ya zama ruwan dare a ƙasar.
Ya bayyana cewa kowace gwamnati mai mutunci sai ta fara da kare jama’arta da inganta walwalarsu.
Ya jaddada cewa tun da gyare-gyare ana yi ne don al’umma, dole ne a yi su da tausayi da jinkai. A cewarsa, “Ko gwamnati ta yarda ko ta Æ™i, gaskiyar rayuwarmu ita ce talakawa suna mutuwa da yunwa, yayin da sauran marasa Æ™arfi ke rayuwa ne kawai a Æ™arÆ™ashin muguwar manufar wannan gwamnati.”