Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta yaba wa al’ummar jihar bisa yadda suka gudanar da bikin Takutaha cikin lumana da tsari ba tare da tashin hankali ba.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce wannan shekarar ta kasance mafi lumana a tarihin bikin Takutaha a Kano, sabanin wasu lokuta da aka saba samun rikice-rikice.
Rundunar ta danganta wannan nasara ga dabarun tsaro na zamani da kuma haɗin kai tsakanin ’yan sanda da al’umma.
Kwamishinan ƴan sandan Kano ya yaba da rawar da shugabannin al’umma, gwamnati, sauran hukumomin tsaro da ƙungiyoyin sa-kai suka taka wajen tabbatar da zaman lafiya.
Tare da jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi tare da yin aiki kafada da kafada da jama’a.
Sanarwar ta kuma shawarci al’umma da su ci gaba da bayar da hadin kai da ’yan sanda ta hanyar sanar da duk wani abin da su ke zargin zai iya kawo barazana ga zaman lafiya.