Masana a fannin abinci sun gargaɗi iyaye da su dena dogara da taliyar yara, wacce aka fi sani da indomi a matsayin abinci.
Masanan sun nuna cewa irin waɗannan abincin ba su da sinadaran gina jiki kuma su na da illa wajen girma da lafiyar yara.
Da ya ke zantawa da PUNCH Healthwise, tsohon shugaban ƙungiyar likitocin abinci ta ƙasa, Wasiu Afolabi ya yi gargadin cewa tabbata indomi na da saukin samu da kuma sarrafawa, amma kuma bata da sinadaran da za su sanya yaro ya samu daidaiton abinci a jikin sa.
Afolabi ya yi bayanin cewa ana yin taliyar indomi ne daga sufaffen hatsi da za su baiwa yaro kuzari kawai a jiki amma ba sa dauke da sinadaran gina jikin.
Afolabi ya yi gargadin cewa dogaro ga indomi kacokan zai iya haifar wa yara rashin lafiya mai tsawo ko gajeren zango.
Ya kuma bada shawarar cewa iyaye su rika hada wa da ganyayyyaki da sauran nau'ikan abinci masu sinadaran gina jiki idan na za su baiwa yara indomi din.