Ministan Sufuri, Said Alkali ya ce aikin titin jirgin-ƙasa mai tsawon kilomita 387 da ake yi daga Kano zuwa Maradi ya kai kashi 60 cikin 100 na kammalawa.
Alkali ya bayyana hakan ne a jawabinsa yayin taro kan harkokin sufurin jirgin ƙasa na Ƙasa da Ƙasa karo na biyu a Abuja.
A cewar sa, gwamnatin taraiya ta fadada aikin har zuwa Dutse ta jihar Jigawa.
Alkali ya baiyana cewa shima aikin layin-dogo na daga zuwa Kano ana daf da kammala shi kuma a kaddamar da shi a watan Disambar 2026.