Matakin hauhuwar farashi ya sauka zuwa
20.12%- NBS
Daga Hafsat Muhammad Abuja
Matakin hauhuwar farashi ya sauka zuwa kashi 20.12 cikin 100 a watan Agusta, in ji Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS).
A rahoton da NBS ta saki a yau Litinin ya nuna cewa matakin hauhuwar farashin kayan abinci ma ya sauka zuwa kashi 1.65 idan aka kwatanta da kashi 3.12 a watan Yuli.
Rahoton ya ce an samu saukar matakin hauhuwar farashin ne da kashi 1.76 idan aka kwatanta da matakin hauhuwar farashi na kashi 21.88 a watan Yuli.