Ina jin daɗin yadda aka fara canja kafafen sada zumunta suka zama dandalin yaɗa addinin Musulunci - Dr Dahir
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi Dakta Dahir Muhammad Hashim ya baiyana jin daɗin da akan yadda ake mayar da kafafen sadarwa daga dandalin yaɗa labaran karya zuwa na yada addinin Musulunci.
A wani sako da ya wallafa Dr Hashim, ya bayyana hakan ne bayan da ya halarci bikin rufe musabakar karatun Alkur'ani mai girma da haɗakar shugaban ƙasa, Maryam Shetti ta shirya a jihar Kano.
A sakon, Dakta Hashim ya yi kira ga a dore da yin ire-iren waɗannan shirye-shirye domin ci gaban addinin Musulunci da al'ummar Musulmi baki ɗaya.
"Na sami damar halartar bikin rufe gasar karatun Al-Kur’ani Mai Girma ta #ReciteWithShetty, wadda Dr. Maryam Shetty ta shirya tare da kulawar Malam Aminu Ibrahim Daurawa.
"Na yi matuƙar farin ciki da ganin yadda ake ƙoƙarin mayar da kafafen sada zumunta daga wurin yada labaran ƙarya da ƙage zuwa muryar yaɗa addinin Musulunci, musamman karatun Al-Kur’ani Mai Girma.
"Ina kira ga masu gudanar da wannan shiri da su tabbatar da dorewarsa, tare da ƙirƙirar wasu shirye-shirye makamantansu don ci gaban al’umma baki ɗaya," a cewar Dr Hashim.