Wata kotun hukunta likitoci a Birtaniya ta saurari karar da aka shigar a kan wani likita mai suna Suhail Anjum, wanda ya bar mara lafiya da ake wa aikin tiyata domin yin jima’i da wata malamar jinya a wani É—aki a Asibitin Tameside, Greater Manchester.
Likitan mai kula da ɓangaren allurar kashe zafin ciwo ya baiyana cewa ya buƙaci ɗan hutu ne, sannan ya roƙi wani abokin aikinsa ya ci gaba da lura da marar lafiyar a lokacin da ake tsaka da aikin tiyata.
Amma maimakon ya É—an sha ruwa ya koma aiki, sai gogan naka ya tafi wani É—akin tiyata inda ya sadu da wannnan malamar jinya.
Wata likita ce ta danno kai cikin dakin, ta ko same su turmi da tabarya suna aikata masha'a, inda bata yi wata-wata ba ta je ta kai rahoton su ga mahukunta.
Lauya Andrew Molloy, wanda ya wakilci hukumar kula da likitoci (GMC),
Yace “Gaskiya ne cewa babu wani lahani da hakan ya haifar ga marar lafiyan a lokacin da Dr Anjum ya bar É—akin tiyatar, kuma an ci gaba da aikin ba tare da wani cikas ba.”
Dr Anjum ya amsa laifin sa, inda ya bayyana hakan a matsayin abin kunya.
Ya shaida wa kotun cewa:
“Abin kunya ne Æ™warai. Ni kaÉ—ai nake da laifi.”
An saka ranar Juma’a domin ci gaba da sauraron shari'ar.