Firaministan Japan, Shigeru Ishiba, ya bayyana murabus dinsa a yau Lahadi, kasa da shekara guda da darewarsa kan mulki bayan shugabantar jam’iyyar Liberal Democratic Party (LDP).
Dalilin murabus din shi ne rashin kyakkyawan sakamakon da jam’iyyarsa ta samu a zabukan majalisun kasar, wanda ya haifar da matsin lamba daga cikin jam’iyyar.
Duk da goyon bayan jama’a a baya-bayan nan, Ishiba ya sha suka daga cikin manyan jam’iyyarsa ta LDP, ciki har da manyan jiga-jigai kamar tsohon Firaminista Yoshihide Suga da Ministan Noma Shinjiro Koizumi, wadanda suka bukace shi ya ajiye aiki.
A yanzu, ‘yan majalisar dokoki da shugabannin yankuna na LDP za su taru a mako mai zuwa domin shirya sabon zaben shugabanci na jam’iyyar.