Rikici ya barke a tsakanin matatar Dangote da Kungiyar Ma,aikatan Mai da Iskar Gas ta Kasa NUPENG
Daga Hafsat Muhammad Abuja 
Kungiyar masu sayar da man fetur ta Najeriya da kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya sun bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani a rikicin da ke tsakanin kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya da matatar man ta Dangote.
 Sai dai kungiyar kwadago ta Najeriya, yayin da ta kuma yi kira da a kawo dauki cikin gaggawa a rikicin, ta zargi matatar dangote da ayyukan yaki da ayyukan kwadago.
Hakan na zuwa ne bayan da kungiyar NUPENG ta bayyana a ranar Juma’a cewa za ta fara yajin aiki a ranar Litinin 8 ga watan Satumba.
Rikicin dai ya ta’allaka ne kan shirin matatar mai na Dangote na shigo da manyan motoci 4,000 masu amfani da iskar gas domin rarraba mai kai tsaye ga ‘yan kasuwa.
 Ko da yake shirin, wanda aka shirya farawa a ranar 15 ga watan Agusta, ya samu jinkiri sakamakon tsaiko a kasar Sin, matatar ta ce za ta fara aiki da zarar manyan motocin sun iso 
 Sai dai a wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar, Williams Akporeha da babban sakataren kungiyar, Afolabi Olawale, suka sanyawa hannu a ranar Juma’a, kungiyar ta NUPENG ta zargi matatar dangote da ayyukan yaki da ’yan kwadago da ke barazana ga rayuwar mambobinta reshen Direbobin Man Fetur da Tanka.
Kungiyar ta koka da yadda mai matatar man, Aliko Dangote, ya dage kan cewa ba za a bar sabbin direbobin manyan motocin da za a shigo da su daga kasashen waje shiga kowace kungiya ba.
  Ta bayyana matakin da cewa cin zarafi ne ga ‘yancin yin aiki da kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999, da kuma keta yarjejeniyoyin kwadago na kasa da kasa da Najeriya ta rattaba hannu a kai.
 NUPENG ta tuna cewa ta gudanar da tarurruka da dama, domin shawo kan Dangote ya sake tunani.