Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida a Saudiyya ta bayyana cewa an zartar wa wata mata mai suna Husn bint Mutib Al-Tuhaimi hukuncin kisa bayan ta kashe mijinta ta hanyar zuba masa gubar acid yayin da yake barci.
Babbar Kotun Ƙoli ce a ƙasar ta tabbatar da hukuncin bayan samun amincewa daga Fadar Sarki Salman bayan da aka gurfanar da matar tare a gaban kotun tare da yanke mata hukuncin.