Bayanai daga Masana'antar Kannywood sun rawaito cewar Gwamnatin Yobe za ta ɗauki nauyin jinyar Malam Nata’ala
Wani makusancin Malam Mato daga Masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood ya bayyanawa Jaridar Raihana, wanda ya nemi a sakaya sunan sa.
Yace "Gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni, ta amince za ta biya dukkanin kuɗaɗen jinyar fitaccen jarumin Kannywood, Malam Nata’ala, wanda ke fama da ciwon daji".
Wanda yace Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Muhammad Lawan Gana ne, ya bayyana haka lokacin da ya kai masa ziyara a gidansa da ke Potiskum.
Kwamishinan ya ƙara da cewa wannan alheri na nuna yadda Gwamna Buni ke tausaya wa jama’arsa tare da taimaka wa masu buƙatar kulawar gaggawa.
Malam Nata’ala ya yi wa Gwamna Buni godiya bisa wannan taimako, inda ya ce hakan zai zama babban sauƙi a gare shi da iyalinsa.
Haka kuma Malam Nata'ala ya bayyana jindadinsa da addu'oi ga Gwamna Mai mala.
Cikin mako da ya bagaba ne, Malam Nata’ala ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa shugaban ƙasar Nijar, ya taimaka masa da kuɗi, sai dai cikin jawabin nasa ya ce bazai fadi adadin kudin da aka bashi, sakamakon kada batagari su biyo shi asibiti su kwace masa kudin.
Amma dai ya bayyana cewar kudade makudai Gwamnatin kasar Nijar din ta bashi.
Wanda shi ma makusancin Malam Mato ya ce tabbas Gwamnatin Nijar ta bada gudunmawar kudade
kimanin Naira miliyan 27 domin ya ci gaba da neman magani, bayan ya nemi taimakon jama’ar gari.
A madadin Jaridar Raihana na yiwa Malam Mato addu'oi samun lafiya.