Gwamnatin jihar Kano ta kammala sayen gidaje 324 da ke Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo daga hannun Pension Funds Trustees kan kudi naira biliyan 4.5, inda aka mika su ga Hukumar Samar da Gidaje ta Jihar Kano domin kula da su tare da sayarwa ga masu sha’awa.
Wannan mataki ya biyo bayan biyan bashin da ke kan gidajen, ciki har da ribar kaso 10 cikin 100 ga Pension Trustees, wanda ya kai naira miliyan 400.
An biya kudin ta hanyar Hukumar Samar da Gidaje, lamarin da ya tabbatar da kare hakkokin masu ritaya tare da bada damar amfani da gidajen yadda ya dace.
A wajen bikin mika gidajen, Manajan Daraktan Hukumar Samar da Gidaje, Alhaji Abdullahi Rabiu, ya bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da samarwa da kuma kula da gidaje masu inganci domin cika bukatar yawan jama’ar Kano da ke ta karuwa.
Ya ce wannan ci gaba babbar nasara ce ga tsarin samar da gidaje a jihar.