Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana kudirin ta na gabatar da buÆ™ata a gaban Majalisar Dokokin Jihar domin sahalewa dokar hana auren jinsi da kuma dakile duk wasu ayyuka da suka shafi wannan al’amari, karkashin tsarin shekarar 2024.
Wannan batu ya fito ne daga bayanin da Kwamishinan Ƙasa da Safayo, Hon. Abduljabbar Umar Garko, ya gabatar wa manema labarai jim kadan bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar a Kano.
A cewar kwamishinan, dokar da gwamnati ke neman sahalewa ta kunshi manufofi uku masu muhimmanci:
1. Kare Addini da Al’adu: Tabbatar da tsaron darajar Musulunci da al’adun Hausawa daga duk wani tasirin da zai iya lalata tsarin su.
2. Tsaron Matasa da Al’umma: Samar da dokar da zata kare jama’a, musamman matasa, daga fadawa cikin ayyuka masu sabawa dabi’a da tsarin rayuwa.
3. Kare Mutuncin Kano: Bayar da kariya ga matsayin Jihar Kano a matsayin cibiyar al’adu da addini a Arewa da Najeriya baki É—aya.
Ya kara da cewa, gwamnatin Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf tana da cikakken shiri na yin aiki kafada da kafada da Majalisar Dokokin Jihar,
Domin tabbatar da samar da ingantattun dokoki da za su tsare rayuwar al’umma, su kuma tabbatar da zaman lafiya, mutunci da dorewar al’adun jama’a.