Gwamnatin jihar Kano ta ce, zata rufe makarantun kudin da aka kama sun kara kudin makaran nan take tare kuma da gurfanar sa su a kotu.
Shugaban Hukumar kula da makarantu masu zaman kansu ta jihar Kano Baba Abubakar Umar Tarauni ne, ya bayyana hakan a ranar Al-hamis din nan yayin da yake ganawa da manema labarai a Kano.
Baba Abubakar Tarauni, ya ce Gwamnati ta dauki wannan matakin ne sakamakon koken da iyayen yara ke yi na karin kudin da makarantun kudin suka yi.
Sannan shugaban ya ce, za su fara rufe makarantun da ke biyan masu kwalin Digiri kasa da Dubu 20 da kuma masu tilasta biyan kudin biki.
Sannan shugaban hukumar Baba Abubakar Tarauni ya ce, ya bukaci iyaye da su dinga biyan kudin makaranta akan lokaci.
Daga karshe shugaban hukumar ya bukaci iyaye da su dinga biyan kudin makaranta akan lokaci.