Gwamnatin taraiya za ta fara karbar haraji daga hannun mata masu zaman kansu
Taiwo Oyedele, shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kuɗi da gyaran dokokin haraji, ya ce kudaden da masu yin karuwanci ke samu za a rika cire musu haraji daga cikin da a ƙarƙashin sabon tsarin.
Oyedele ya yi wannan bayani ne a wani faifen bidiyo da ya wallafa a shafin X a jiya Litinin, inda ya kawo misalan hanyoyin samun kuÉ—in da ake sanya wa haraji.
Masanin harajin ya bayyana cewa sabbin dokokin ba sa bambanta tsakanin hanyar halal ko ta haram wajen samun kuÉ—i ba abin da suke dubawa kawai shi ne ko kuÉ—in ya fito daga sayar da kaya ko kuma wani aiki da aka yi a ka biya.
“Ga wani misali mai tsanani… idan wani mutum yana yin dadiro, suna neman maza su kwanta da su. Ka sani wannan aiki ne, za a É—auki haraji a kai,” in ji shi.
“Abu É—aya game da dokar haraji, ba ta bambanta ko abin da kake yi halal ne ko ba halal ba, ma ba ta tambayarka hakan ba.
“Abin da take tambaya shi ne, shin kana samun kuÉ—i? Shin ka samu kuÉ—in ne ta hanyar aikin da kayi ko sayar da kaya? Idan haka ne, sai ka biya haraji.”
A gefe guda kuma, Oyedele ya ce kuÉ—aÉ—en kulawa da ake aika wa ‘yan uwa, abokai ko ma baÆ™i ba a É—auke su a matsayin abin da ake ciro haraji akai, domin ana É—aukar su kyauta ce.
“Ka samu wani adadin kuÉ—i sannan ka aika wa É—an uwanka, É—an’uwanka ko ma wani baÆ™o kuÉ—i don kulawa, ba kome ba ne. Idan kuÉ—in da kake aikawa kyauta ne, ba don sun yi maka wani aiki ba, to wannan kyauta ce. Muna kiran shi mu’amala ba ta musayar abu. Wannan ba abin da za a harhaÉ—a da haraji ba ne,” in ji Oyedele.