Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta karbe wa Afrika ta Kudu maki 3
Hukuncin ya ce an bai wa Lesotho maki uku a wasan da ci 3-0, sannnan an ci tarar Bafana Bafana kwatankwashin kusan naira miliyan 18.
Wannan na zuwa ne bayan da Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ta ƙwace makin nata da ta yi amfani da ɗan wasan da aka dakatar, Teboho Mokoena a karawarsu da Lesotho a watan Maris.
Yanzu kenan rukunin C na neman shiga kofin Duniya ya zama Benin a farko da maki 14, sai Afrika ta Kudu a mataki na biyu da maki 14 ita ma.
Sai kuma Najeriya mataki na uku da maki 11, inda ya rage wasanni biyu a kammala wasannin share fagen shiga gasar cin kofin duniya a badi.