Kungiyar Izala ta ce ta hada fiye da Naira Miliyan 170 daga Fatun Layya
Kungiyar Izala mai shalkwata a Kaduna ta ce ta tara kuÉ—i har naira 170,974,512.50 daga gudunmuwar fatun layya da ta samu a babbar sallar shekarar 1446/2025.
Shugaban ƙungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ne ya karɓi rahoton kwamitin tattara fatun layyar, ƙarƙashin jagorancin Malam Lamara Azare yayin taron majalisar ƙolin ƙungiyae da aka gudanar a dakin taro na JNI da ke Kaduna ranar Asabar, 6 ga Satumba, 2025.
Sanarwar ta bayyana cewa Kaduna ce ta fi bayar da gudummawa da naira miliyan 23, sannan Kebbi ta biyo da naira miliyan 21 da kuma Sokoto da naira miliyan 18. Bauchi, Zamfara, Adamawa, Neja da Katsina suma sun bayar da kuɗaɗe masu yawa, yayin da sauran jihohi suka biyo baya da ƙananan adadin kuɗi.
Kungiyar ta ce jimillar kuÉ—in da aka tattara daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja ya kai naira miliyan 170.9.