Rundunar ƴan sandan Kano ta kama mutane 9 bisa rikicin da ya faru a Garin Garko da ke Jihar
Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta cafke mutane 9 da ake zargi da hannu a tarzomar da ta barke a ƙaramar hukumar Garko bayan rahoton zargin kisan kai.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 6 ga Satumba, 2025.
Sanarwar ta ce gungun ɓatagari sun kai farmaki ofishin ƴan sanda na Garko, inda suka ƙona motar sintirin rundunar, sannan suka lalata wasu motoci uku mallakin Hisbah ta ƙaramar hukumar, tare da jikkata jami’an ƴan sanda uku.
Sanarwar kuma ce wani mutum ya rasu yayin tarzomar, wasu uku kuma sun jikkata, yayin da ake ci gaba da bincike domin kama sauran waɗanda suka gudu.