Fitaccen mawakin nan Akon na fuskantar wani babban sauyin rayuwa yayin da matarsa, Tomeka Thiam, ta shigar da takardar neman saki bayan kusan shekaru talatin da aure.
Jaridar People ta ruwaito a yau Asabar cewa, takardun kotu da aka shigar a Fulton County, Georgia, a ranar 11 ga Satumba, 2025, sun nuna cewa Thiam na neman a kawo ƙarshen auren ne saboda “rigingimu da ba za a iya sulhunta wa ba.”
A watan gobe ne dai ma’auratan, waɗanda ke da ƴa mace guda ɗaya, za su yi bikin cika shekaru 29 da aure.
A cikin bukatarta, Thiam ta nemi hakkinta na kula da ƴar t su daga bangaren doka tare da Akon, amma ta roƙi kotu da ta bar ƴar wajen ta don kulawar yau da kullum, sannan a bai wa Akon damar ziyartar ta.
Haka kuma ta nemi kotu da ta baiwa Akon umarnin ba ta kuɗaɗen ciyarwa da kulawa da ita da ƴar ta su, tare da roƙon kotu ta ƙi amincewa da duk wata buƙatar Akon da zai iya gabatarwa a wannan fanni.
Wannan neman saki na zuwa ne a daidai lokacin da Akon, mai shekara 51, ke ci gaba da nuna ra’ayinsa a fili kan auren mace fiye da ɗaya, wani abu da ya daɗe yana danganta shi da al’adarsa.