Ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa ta dakatar da yajin aiki
Daga Hafsat Muhammad Abuja
Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin gargadin da ta fara kwanaki biyu da suka gabata.
Shugaban kungiyar, Tope Osundara, ya shaida wa TheCable a ranar Lahadi cewa an umarci likitocin da su koma bakin aiki nan take.
“An dakatar da yajin aikin,” in ji Osundara a wata hira ta waya.
“An cika mana wasu daga cikin bukatunmu. Gwamnati ta yi alkawarin duba sauran matsalolin.
“Mun yi haka ne a matsayin alamar kyakkyawar niyya, tare da taimaka wa ‘yan Najeriya da ke neman kulawar lafiya a cibiyoyinmu daban-daban.”
Osundara ya bayyana cewa likitocin za su sake nazarin matakan da gwamnatin tarayya ta dauka kan sauran bukatun da ba a biya musu ba.
Ya ce bukatun da har yanzu ba su samu kulawa kai tsaye ba sun hada da bashin albashi da suke bi da kuma rage darajar takardun shedar mamba daga West African Colleges of Physicians and Surgeons da Majalisar Likitoci na Najeriya (MDCN) ta yi.
Shugaban NARD ya kara da cewa sauran bukatun sun hada da karancin ma’aikata da kuma gaggauta fitar da daftarin da aka gyara na tsarin albashin likitoci daga Hukumar Albashi, Kudaden Shiga da Alawus (NSIWC).
Likitocin sun sanar da fara yajin aikin gargadi na kwana biyar a ranar Juma’a, lamarin da ya kawo nakasu ga ayyukan asibitocin tarayya a fadin kasar.