NAHCON ta ce ta rage kuɗin aikin Hajji duk da zarge-zargen cin hanci
Daga Hafsat Muhammad Abuja
Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce hukumar ta samu nasarar rage kuɗin aikin Hajji ta hanyar samun rangwame daga masu ba da masauki da wurare a Saudiyya, da kuma sauya tsarin biyan kuɗi daga dalar Amurka zuwa Naira.
Farfesa Abdullahi ya bayyana cewa da ba a ɗauki waɗannan matakan ba, kuɗin aikin Hajji na bara zai iya haura Naira miliyan 11 ga duk mutum guda.
Ya ce hukumar ta samu rangwamen Riyal 720 a wuraren Mina, Arafat da Muzdalifa, da Riyal 200 a Madina, da kuma Riyal 303 kan kuɗin sufuri daga Makka zuwa Muna.
Ya kara da cewa an kuma sauya tsarin karɓar kuɗin mahajjata daga katin ATM zuwa kuɗi kai tsaye domin sauƙaƙa musu, sannan aka faɗaɗa tsarin ajiyar kuɗin Hajji daga banki guda zuwa bankuna huɗu.
Game da binciken da EFCC ke yi kan hukumar, Usman ya ce NAHCON ta kasance cikin tsangwama daga cikin gida saboda hassada da son zuciya.
Ya ce duk da haka, hukumar ta gudanar da aikin Hajji mafi nasara tun kafuwarta, kuma babu wanda ya yi ƙorafi.
Ya bayyana cewa a bara NAHCON ta mayar wa mahajjata N5.3bn da aka biya don sanyaya iska a Mina da Arafat amma ba a samu ba.
Kowane mahajjaci ya samu kusan N60,000 a matsayin kuɗin da aka mayar masa.
Shugaban ya karyata zarge-zargen cewa ya fifita wasu ko kuma ya yi amfani da mukaminsa wajen amfanar da danginsa, yana mai cewa ya kawo ƙwararru biyu ne kawai domin ƙwarewarsu.
Ya ce hukumar ta ci gaba da inganta walwalar mahajjata, musamman a Madina inda aka samu masauki mafi kusa da Harami fiye da kowanne lokaci, sannan ya yi kira ga masu niyyar zuwa Hajji da su biya kuɗinsu da wuri domin samun sauƙi.