A karon farko tun bayan kafa hukumar shirya jarabawar NECO shekaru 25 da suka gabata, Jihar Kano ta hau kan gaba a jerin jihohin Najeriya masu nasara a jarabawar NECO ta shekarar 2025.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta nuna cewa Kano ta kasance ta farko, inda ta baro Jihar Lagos wacce ta zo ta biyu da Oyo wacce ta tsaya a mataki na uku, yayin da sauran jihohi suka biyo baya.
Wannan gagarumar nasara ta samo asali ne daga shirin gyaran fannin ilimi da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya dauki alwashin aiwatarwa tun daga zuwansa kan karagar mulki.
A cewar masana, wannan matsayi da Kano ta kai shi ya zama shaida kan jajircewa da kuma kudirin gwamnan wajen inganta tsarin ilimi a fadin jihar.
A halin yanzu, an taya Gwamnan Kano murna bisa wannan tarihi da ya kafa, wanda ya nuna jihar ta fara cin gajiyar kudirin inganta ilimi a karkashin jagorancinsa.